A rahoton da Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya samu daga Sari, Iran, an gudanar da bikin buɗe sabuwar shekarar karatu ta makarantun addini (Hauza) na lardin Mazandaran a safiyar yau, tare da halartar Hujjatul Islam wal Muslimin Shabzandedar, sakataren Majalisar Koli ta Hauzozin Ilimi na ƙasar Iran, da kuma Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammadi La'ini, Wakilin Waliyyul Faƙih a Mazandaran.
An gudanar da wannan biki ne a Makarantar Hauzar Imam Sadik (A.S) da ke Kutenai, a birnin Qa'imshahr.
A yayin jawabinsa, wakilin mutanen Mazandaran a Majalisar Kwararrun Jagoranci ya jaddada cewa aikin Hauzozin Ilimi shi ne fahimtar maganar Allah daidai, sannan a isar da ita ga jama'a.
Limamin Juma'ar birnin Sari ya tunatar da ayoyin Alƙur'ani daga Suratul A'araf, inda Allah Madaukakin Sarki yake cewa:
قَالَ يَا مُوسَى إِنِّي اصْطَفَيْتُكَ عَلَى النَّاسِ بِرِسَالَاتِي وَبِكَلَامِي فَخُذْ مَا آتَيْتُكَ وَكُنْ مِنَ الشَّاكِرِينَ (144) وَكَتَبْنَا لَهُ فِي الْأَلْوَاحِ مِنْ كُلِّ شَيْءٍ مَوْعِظَةً وَتَفْصِيلًا لِكُلِّ شَيْءٍ فَخُذْهَا بِقُوَّةٍ وَأْمُرْ قَوْمَكَ يَأْخُذُوا بِأَحْسَنِهَا ۚ سَأُرِيكُمْ دَارَ الْفَاسِقِينَ (145)
Allah ya ce wa Annabi Musa (A.S): “Ya Musa! Lallai Na zaɓe ka a kan mutane domin isar da saƙonnina da kuma maganata gare ka. Saboda haka, ka karɓi abin da Na ba ka, kuma ka kasance daga masu godiya(144). Kuma Mun rubuta masa a kan alluna wa'azi da bayanin duk abin da ake bukata, sannan muka ce masa ya riƙe su da ƙarfi, kuma ya umurci mutanensa su riƙe mafi kyawun abin da ke cikinsu.”
Hujjatul Islam Muhammadi La'ini ya bayyana cewa Allah Madaukakin Sarki Ya zaɓi malaman addini domin su fahimci saƙonsa yadda ya kamata, sannan su isar da shi ga jama'a.
Ya ce: “A takaice, matsayin Hauzozin Ilimi shi ne fahimtar maganar Allah Madaukakin Sarki da kuma isar da ita ga mutane.”
Wakilin Waliyyul Faƙih a Mazandaran ya ƙara da cewa domin mutum ya fahimci maganar Allah da saƙonsa yadda ya kamata, wajibi ne ya kasance mai godiya ga wannan babbar ni'ima.
Ya bayyana cewa kafin mutum ya cancanci wannan matsayi, dole ne ya fara samun ƙwarewa da cancanta, sannan ya gina kansa domin hidimar Allah Madaukakin Sarki.
Limamin Juma'ar Sari ya ce makarantun addini an zaɓe su ne domin wannan babban aiki. Saboda haka, ya ce dole ne ɗaliban Hauza su kula da gina kansu yadda ya kamata, tare da samun ingantacciyar tarbiyya da tsarkake zuciya.
Hujjatul Islam wal Muslimin Muhammadi La'ini ya kuma yi ishara da nau'o'i biyu na sakamakon da makarantun addini ke bayarwa. Ya ce wasu daga cikin ɗaliban da suka kammala karatu a waɗannan makarantu suna ci gaba zuwa manyan Hauzozin Ilimi domin zurfafa karatunsu, yayin da wasu kuma daga cikin waɗanda suka yi karatu a irin waɗannan makarantu suka kai ga matsayin shahada.
Ya bayyana cewa wannan makaranta ta Imam Sadik (A.S) ta riga ta samar da ɗalibai da waɗanda suka kammala karatu 57 da suka samu shahada, yana mai cewa ya kamata a yi musu sallama da gaisuwa saboda irin matsayin da suka kai.
Ra'ayinka